28 Satumba 2019 - 04:38
​Majalisar Wakilan Amurka Na Hankoron Tsige Trump

Majaliasr wakilan kasar Amurka ta zargi shugaban kasar Donald Trump da aikata ba daidai ba, ta hanyar yin wata magana ta sirri da shugaban kasar Ukraine domin yin kutse a cikin harkokin zaben kasar.

(ABNA24.com) Majaliasr wakilan kasar Amurka ta zargi shugaban kasar Donald Trump da aikata ba daidai ba, ta hanyar yin wata magana ta sirri da shugaban kasar Ukraine domin yin kutse a cikin harkokin zaben kasar.

Jaridar New York Times ta buga rahoton cewa, majalisar wakilan ta Amurka ta zargi fadar White House da boye bayanan da suka gudana a tsakanin Trump da kuma shugaban kasar Ukraine.

Sai dai hukumomin leken asiri an kasar ta Amurka sun bayyana cewa sun samu bayanan wadanda aka nada ta hanyar sauti, a lokacin da Trump yake zantawa da shugaban na kasar Ukraine, inda a ciki yake matsa lamba kan shugaban na Ukraine da ya gudanar ad wani bincike kan Joe Biden, wanda shi ne dan takarar jam’iyyar Democrat da ake ganin zai iya zame ma Trump barazana a zabe mai zuwa.

Wannan ne yasa shugabar majalisar wakilan kasar ta Amurka Nancy Pelosy ta bayyana cewa, majaliasar ta gabatar da wani daftarin kudiri na yin kiranye ga Trump domin bayar ad baasi kan batun, wanda ka iya kaiwa ga tsige shi.

A halin aynzu dai shugaban na Amurka na cikin mawuyacin hali, saboda rashin sanin abin da zai kai ya komo dangane da batun tsige shi, wanda kuma idan har kudiri ya yi nasara, to kuwa za a tsige Donald Trump daga kan shugabancin Amurka, kafin wa’adinsa na farko ya kare.




/129